Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Najeriya (RIMAN), ta ce matakin dage haramcin shigo da wasu kayayyaki daga kasashen waje ciki har da shinkafa babbar barazana ce a gare su.
Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya shaida wa kafar BBC cewa, a gaskiya wannan mataki ya zame musu kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya sun sanya kudadensu sun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar Æ™asa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, “sai kawai mu ji an ce an dage haramcin shigo da shinkafar waje.”
“A yanzu mu matakin da za mu dauka shi ne za mu yi magana da gwamnati mu ba ta shawara, sannan mu saurara mu ji ko za su saurari kokenmu.”
Peter Dama, ya Æ™ara da cewa,” Idan har ana so a samu saukin tsadar shinkafa a kasa to sai a rage kudin man fetur da na kayan aikin gona, da kuma ba wa manoma taimakon da zai bunkasa nomansu.”