Yan majalisar wakilai sun amince a bude iyakokin dake Arewa, amma a rika sa ido, sannan ba a yarda da bude iyakokin da ke kudu ba.
Tunda fari, Aliyu Sani Madakin Gini mai wakiltar Dala a majalisar ne ya bijiro da batun a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce mutanen Arewa su na samun ciniki sosai tsakanin al’ummar Nijar, Mali, Chad da Kamaru a Maigatari, Kongwalam da Illela.
Dan majalisar ya ƙara da cewa, rufe iyakokin ya jawo kiyayya tsakanin wadannan al’umma da ke makwabtaka da juna, sannan kuma an samu karuwar fasa kauri da sauran laifuffuka
Tun watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta da makwabciyar ƙasa Nijar, sakamakon juyin mulki da sojoji su ka yi a jamhuriyyar.
Aliyu Sani Madakin Gini dai dan majalisa ne daga jihar Kano, wanda yake wakiltar karamar hukumar Dala, kuma shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.