A wani rahoto da muke samu na wata mata mai suna Angela cewa mijin ta ya dirƙa mata saki biyo bayan yadda ciyar da ita ya gagareshi.
Mijin nata mai suna Daniel ɗan asalin Jihar Imo ya shaida wa Manema Labarai a ranar laraban da ta gabata cewa shi yayi iya ƙoƙarinsa na wurin ɗaukan nauyin matarsa kuma yayi kira ga iyayen ta da suma su zo domin haɗa kai dan ciyar da ɗiyar su amma suka yi kunnen Uwar Shegu da shi.
Daniel dai ya auri Angela ne a matsayin bazawara bayan rabuwar ta da mijinta na lalle wanda bai bayyana dalilin rabuwan nasu ba.
Bugu da kari ya ƙara Bayyana wa manema labarai cewa a mako ɗaya kawai matar tana cinye rabin buhun Masara ita kaɗai, idan kuma shinkafa za'a girka ita kaɗai kawai take tada tiya ɗaya da rabi daga safe zuwa dare, ɓangaren ruwa kuma tana iya shanye ruwa leda biyar na fiyo wata Cikin kwana Uku rigis, kifi ko Nono kuma ba'a maganarsu, a bisa waɗannan dalilan yasa mijin nata ya haƙura da ci gaba da zama da ita.”
Inda yace can gasu gada.