ÆŠaliban Makarantar kwalejin Annur dake rangaza a kano sun gudanar da babban taro don taya malaman su murnar zagayowar ranar malamai ta duniya.
Ranar malamai ta duniya rana ce da aka ware a ranar 5 ga watan octoban shekarar 1960 a birnin Newyork dake Amurka. Tun daga wannan rana ake gabatar da biki na musamman domin a duk ranakun biyar ga watan octobar kowace shekara.
Ɗaliban sun gudanar da ɗan gajeran wasan kwaikwayo mai ɗauke da darasi kan muhimmancin girmama malamai basu haƙƙunan su wanda bai taka kara ya karya ba.
Mal. Sani Namadi shi ke zama DEAN na sashen EDUCATION a Kwalejin Annur yayi mana ƙarin haske tare da bayyana farin cikin sa duba da yadda waɗannan ɗalibai suka shirya taro na musamman da kansu don taya su murnar zagayowar wannan rana tare da karramasu.
Suma a nasu bangaren ɗaliban Aisha Muhammad Hadi wadda ta gabatar da muƙala kan muhimmancin malamai tace ba don komai yasa suka haɗa wannan taro ba sai don su ƙarfafa musu gwiwa wajen cigaba da aikin alkhairi na koyar dasu da suke yi dai-dai fahimtar su kuma iya bakin ƙoƙarin su.