Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano tace Cikin Kwanaki Talatin Da Shida 36 Rundunar tayi Nasarar cafke wasu mutane da ake zargi kan mabanbanta laifufuka daban-daban.
Wannan na zuwa ne ta wata takarda da Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Kanon SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai, Inda yace Rundunar 'Yan Sandan karkashin Jagoranci Kwamishinanta CP Muhammad Hussain Gumel ta kama ba mabanbanta laifuka da daban-daban aciki da wajen Jihar Kano.
1. 'Yan Fashi da Makami su Ashirin Da Takwas (28).
2. Barayin Mota su Takwas (8).
3. Masu Garkuwa da Mutane su Takwas (8).
4. Dillalan Kwaya su Biyar (5).
5. Barayin Baburan Adaidaita Sahu su Uku (3).
5. 'Yan Danfara su Uku (3).
6. 'Yan Daba da Makami su Goma Sha Bakwai (17).
7. Barayin su Goma Shashida (16).
Kayan da aka kama sun hadar da:
1. Bindiga Kirar AK-47 daya 1, Bindiga Kirar Dobil Baraid daya 1, Bindiga Kirar Fisol daya 1, Bindigar gargajiya Kirar AK-47 daya 1, Bindiga Kirar ta gargajiya data wasan yara Guda Biyu (2).
2. Motoci Goma (10), Baburi din Adaidaita Sahu Guda Uku (3), Babura masu kafa Biyu Guda Takwas (8).
3. Shanu Guda Uku (3).
4. Rafa din Kudin Kasar Indiya Dari Uku Da Sittin Da Takwas (368).
5. Kwalaben Magannin Allurar da masu shaye-shaye suke amfani da ita Guda Hamsin Da Uku (53).
6. Magannin Diazepam Guda Dari Da Sittin Da Bakwai (167).
7. Kwayoyin Exol Guda Dari Biyu Da Saba'in Da Biyar (275).
8. Wukake Kirar Adda, Gariyo, Da dangogin su Guda Talatin Da Uku (33).
9. Buhun huna Guda Biyar (5) dauke da Kebulwaya.
10. Dalar Amurka Guda Tamannin Da Biyar (85).
11. Wayoyin Hannu Guda Dubu Daya Da Goma Sha Bakwai (1017).
12 Computer ta hannu Laptop Guda Hudu (4).
13. Katin cirar kudi na ATM Guda Bakwai (7).