Rundunar dake Bada Kariya ga Fararan Hula da Dukiyoyin su ta Kasa Reshen Jihar Kano Civil Defence tayi nasarar kama wasu mata guda 2.
Wadanda ake zargin su da bude gidajen mutane da almakashi domin yin sata.
Rundunar ta kuma kama mata 6 da ake zargin su da sayan kayan satar.
Rundunar tace da zarar ta kammala binciken wadanda ake zargi zata mikasu gaba domin su girbi abinda suka shuka.