Mai magana da yawun Rundunar 'Yan sandan Jihar, ASP Mahid Abubakar, ya ce sun samu rahoto daga wani mutum mai suna Muhammad Abdullahi, mai shekara Arba'in Da Biyar 45, da ya ce wani mutum ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa.
ASP Abubakar, ya ce rundunar 'yan sandan toni ta tura jami'anta da ke yankin Pantami, inda lamarin ya faru, takuma samu matar mai shekara Hamsin Da Takwas 58 kwance cikin jini.
Daga nan aka garzaya da it's zuwa Babban Asitibin Koyarwa na Jihar Gombe, matar mai suna Aishatu Abdullahi, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Kakakin Rubdunar 'yan sanda na Jihar ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da jami'an tsaron ke tuhumarsa.
''Ya bayyana yadda ya lallaɓa ya shiga ɗakin matar domin neman sifanarsa da ya ce ta ƙwace masa. bayan da ta shiga ɗakin ta same shi, sai ta tambaye shi dalilin shigarsa ɗakinta, amma ya ƙi ficewa daga ɗakin, a maimakon haka sai ya far mata, ya shaƙe ta tare da kashe ta da wuƙa, daga nan ya yi ficewarsa, ya bar wuƙar da rigarsa da jini ya taɓa, amma kuma ya fita da sifanar", kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan ya bayyana.
ASP Abubakar, ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne da taimakon wani matashi mai kimannin shekara 17.
Wanda shi ma rundunar ta kama shi, sai dai ya musanta hannu a aikata laifin.