Rundunar 'Yan Sandan Kano tayi nasarar cafke wasu matasa 'Yan Daba su 29 a ranar bikin Takutaha.
Haka kuma an gano wukake masu kaifi 19, Almakashi 2, Karfe 2 (Dan Bida) da wasu miyagun kwayoyi.
Kwamishinan 'Yan Sandan Kano CP Muhammad Hussain Gumel ya yabawa Al'ummar Jahar Kano masu san Zaman Lafiya dama goyon Bayan da hadin kai da suke bawa Rundunar
A bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda. IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM zuwa ga dukkan rundunonin ‘yan sanda da tsare-tsare don tabbatar da gudanar da taron Mauludin Takutaha a fadin kasa baki daya tare da aiwatar da aikin ‘yan sanda da samar al'umma ingantaccen tsaro wanda Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano a kokarinta na ganin ta kakkabe batagari a fadin Jihar Kano dama Kasa baki daya.
Na kiyaye doka da oda, inda Hukumar ta kaddamar da ayyukan sharar fage a wasu lunguna da sako na jihar wanda a lokacin taron Takutaha aka gudanar tsakanin 03/10/2023 da 05/10/2023 jimillar mutane ashirin da tara (29) da ake zargin sun yi kaurin suna.