Ina kara kira ga al'ummar kura/garun malam wajen kara tashi tsaye dan cigaba da gabatar da rokon Allah wajen samun nasarar yayan mu Hon Yusuf Datti da babanmu Alh Abba Kabir Yusuf Ubangiji ya basu nasara dama daukacin yan jam'iyyar mu mai albarka ta NNPP.
Lallai Ubangiji yana tare da bayinsa masu hakuri, al'umma kucigaba da hakuri da juriyar duk wani dan jam'iyyar hammaya da zaice bamu da nasara agaban kotu, wannan abu shiftun gizo ne domin anriga andorasu akan igiziyar zato na "Is Coming" In Sha Allah mune muke da nasara,
Duniya ma ta tabbatar da cewar duk wanda yasamu nasara a karkashin inuwar jam'iyyar NNPP yayi sahihin zabe, domin kuwa bamu da gwamnatin sama ko ta kasa, bamu da jami'an tsaro amma Allah ya dubemu yace mune, yau kuma sunfito sunce bamu bane, toh da Allah muka dogara kuma Hon Yusuf Datti yabi duk wata doka wajen ajiye aikinsa, wannan wata makarkashiya ce da aka shirya mana kuma In Sha Allah nasarorin mu duk zasu tabbata.
Ina godiya ga al'ummar karamar hukumar kura da garun malam dama dukkan masoya Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso domin da bazarsa muke rawa Allah yabamu nasarorin mu duk kan su.