Sheik Lawan Triumph, ya shigar da ƙarar babban mai taimakawa gwamnan Kano a bangaren wayar da kai akan siyasa, Hon Anas Abba Dala, a gaban kotun majistret mai lamba 60, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Tijjani Sale Minjibir, bisa zargin kalaman tunzuri a kansa.
Bayan an karanta masa ƙunshin tuhumar kamar yadda lauyan gwamnati, Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya bukata, Anas Abba Dala ya musanta zargin.
Daga nan aka bada beli kamar yadda lauyansa ya nema, kuma lauyan gwamnati baiyi suka ba,
A karshe Alƙali ya sanya ranar 3 ga watan Nuwamba shekarar da muke ciki domin cigaba da sauraron ƙarar.