Tubabben Dan Daba mai suna "Chile Mai Doki" ya zama "Constabulary"
Idan jama'a basu manta ba a watannin baya ne Rundunar 'Yan sandan Kano suka bada shelar wasu matasan 'yan daba.
Wadanda wannan matashi Chile Mai Doki yana daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuka.
Ya koma mika kansa zuwa Babbar Helikwatar Rundunar 'yansandan Kano ta "Bamfai" sai kuma gashi bayan tuba dayayi da aikata laifin daba yanzu ya koma mai kama masu aikata laifuka.