Hukumar kwastam a Najeriya ta ce tasamu nasarar kama duro Dubu Daya Da Dari Shida 1,600 na tumatir É—in da ya lalace wanda aka sanya cikin wasu kwantenoni guda 20 a Jihar Legas.
An kama kwantenonin ne a tashar jiragen ruwan Legas, tare kuma da cafke wani mutum guda da ake zargi da shigo da su.
A cewar shugaban hukumar ta kwastam, Adewale Bashir, ya ce ana zargin kwantenonin mallakin wani kamfani ne mai suna Nikecristy Investment Limited.
Ya ce jami'ansu ne da ke sintiri ne suka samu nasarar cafke kwantenonin guda 20, waÉ—anda daga bisani aka gano cewa suna É—auke da tumatirin da ya lalace, wanda kuma zai yi wa mutane illa idan suka yi amfani da shi.
Ya ƙara da cewa kwantenonin da aka shigo da su daga ƙasar Sifaniya, za'a biya musu kuɗin fito naira Miliyan Dari Da Goma Sha Shida Da Digo Biyu 116.2
Ya ce zuwa yanzu kwantenonin na karkashin kulawar Hukumar sa har sai bayan an kammala bincike.