Ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen jihar kano wato Association Of Nigerian Autthors (ANA) tayi sabon shugabanni.
Zaben ƙungiyar ya gudana ne yayin gabatar da guda cikin manyan taruka data saba gudanarwa duk ƙarshen wata. inda aka zabi Dr. Murtala M. Uba wanda malami ne a sashen ilimin nazarin ƙasa wato (Geography) jami'ar Bayero a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.
yayin gabatar da jawabin godiya Dr. Murtala yace zasu jagoranci wannan ƙungiya izuwa tafarki mafi dacewa ta kowane bangare tare da haɗin kan mambobin ta musamman shugabannin da suka gabata duk da cewa tun kafuwar ƙungiyar ake ta ƙoƙari wajen ganin an kai ta mataki wanda duniya zata yaba mata duba da manyan masana da ƙwararru a fannin ilimi da take dashi amma haƙan ta yaci tura.sai dai a wannan lokaci na shugabancin su zasu tabbatar da cewa ƙungiyar marubuta a jihar kano ta zama guda cikin manyan ƙungiyoyi da za ayi alfahari da ita. shima sabon PRO Hausa na wannan ƙungiya ta ANA Bashir A Bashir (Influencer) ya jaddada aniyar su ta tabbatar da cewa kungiyar marubuta ta zama zakaran gwajin dafi wajen kawowa al'ummar jihar kano cigaba musamman bangaren ilimi da rubuce-rubucen da zai canzawa matasa maza da mata tunani mai amfani, duk da cewa gwamnati bata tuna su a matsayin masu baiwa al'ummar jihar kano gudunmawa wajen kawo sauye-sauye a zamantakewar al'umma.
Taron ya samu halartar manyan malamai daga manyan jami'o'i a ciki da kewayen ƙasar nan.
Sauran sabbin masu muƙaman sun haɗar da:
1. Chairman: Dr. Murtala M. Uba
2. Vice Chairman: Kamilu Dahiru Gwammaja
3. Secretary: Ibrahim M. Indabawa
4. Ass. Secretary: Aliyu Abdullahi (Abal Hassan)
5.Treasurer: Sadiya Garba
6. Fin. Secretary: Hassan Ibrahim Gama
7. PRO Hausa: Bashir A. Bashir (Influencer)
8. PRO English: Abba Musa Idris
9. Welfare Officer: Sani Scholar
10. Auditor I: Ayyuba Muhammad Danzaki
11. Auditor II: Aisha Aliyu Jibril
12. Legal Adviser: Jibrin Adamu Jibrin Rano
Ex-officio
13. Zubairu M. Balannaji
14. Mukhtar A. Gandu
15. Mazhun Idris
16. Tijjani M. Musa