Allah Ya yiwa Babban mai taimakawa gwamnan Jihar Katsina kan harkokin karatun Addinin Musulunci (SSA Islamic Education) Dr. Shamsu Abubakar rasuwa.
Marigayi Dr. Shamsu Abubakar, ya rasu ne sakamakon haÉ—arin mota da ya rutsa da shi akan hanyarsa daga Jihar Katsina zuwa Jihar Kaduna.
Kafin rasuwar Dr. Shamsu Abubakar Malumfashi, malami ne a jami'ar UMYUK da ke jihar Katsina.
Anyi jana'izarsa, yau Talata a Masallacin Sultan Bello da ke Jihar Kaduna, bayan kammala sallar la'asar.