An binne gawar jarumar Fina-finan Hausa Hajia Binta Ola a jihar Katsina
Marigayar Hajia Binta Ola ta rasu ne daren Jiya Talata 03-10-2023 a daidai lokacin da take tsaka da shire shiren gudanar da Maulidi a gidan ta kamar yadda ta saba yi a kowace shekara.
Kamar yadda Katsina Reporters ta rawaito cewar, kafin rasuwar Hajia Binta Ola, cikin daren sai da ta harhaɗa ƙyaututtuka da Abinci na Maulidi da za a rabawa jama'a a wayewar yau Laraba 04-10-2023.
Matuwar Hajia Binta Ola ta girgiza masana'antar fina-finan Hausa da kuma al'ummar jihar Katsina.
An shedi Binta Ola a matsayin mutunniyar kirki mai son jama'a da taimakon addini.