Ƙungiyar (CIPP), MERCY CORPS Tare da haɗin gwiwar League for Social Protection Against Drug Abuse (LESPADA) sun gudanar da taron kwana guda na manyan masu ruwa da tsaki kan tasirin amfani da miyagun ƙwayoyi ga zaman lafiya da rikici.
Taron wanda ya gudana a ranar Alhamis, a Tahir Guest Palace, yayi maraba da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da samar da hanyoyin magance shan miyagun kwayoyi da maza da mata a cikin al’umma.
A jawabin maraba da Babbar Daraktan LESPADA, Amb. Maryam Hassan ta bayyana cewa an shirya taron bitar ne domin fahimtar illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yadda za'a shawo kan matsalar.
Ta kara da cewa: “Mun taru a yau a matsayinmu na masu hannu da shuni domin tattaunawa kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“Shaye-shayen muggan kwayoyi ya zama kalubale a cikin al’ummarmu, don haka dole ne mu nuna kudurin hadin gwiwa don fahimtar juna, mu fuskanta sannan kuma mu nemi mafita mai zurfi.
"Tare za mu iya bincikawa tare da tuntuɓar juna domin samun matsaya ɗaya, ta yadda haƙan mu zai cimma ruwa''.
Jami'ar kungiyar agaji ta Mercy Corps (CIPP) Halima Kassim Usman ta bayyana cewa akwai bukatar a samar da tsaftar muhalli domin tsaftace al’umma da kuma kawar da shan miyagun kwayoyi.
“A CIPP, muna da wani tsari da ke lura da abubuwan dake faruwa a cikin al’umma ta hanyar wayar da kan jama’a kafin faruwar lamarin.
“Wasu daga cikin tsarin sun haɗa da; masu sa ido kan zaman lafiya na al’umma, mata suna gina shawarwari, ƙungiyoyin tattaunawar mata masu mahimmanci, da kuma masu kafa tushe da masu shiga tsakani.
A wajen gabatar da kasida, Dakta Fatima Sani ta gabatar da kasida kan ‘sakamakon illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da mata ke haifarwa a rikice-rikicen al’umma da samar da zaman lafiya a jihar Kano, ta bayyana cewa: “Shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin mata shine ummul aba'isin shigar al'ummar wannan zamani cikin sabon bala'in da ba'a taba tsammani ba" wanda ya haɗar da:
“amfani da kwayoyi da suka saba wa doka.
"Shaye-shayen miyagun kwayoyi ga mata na iya zama babbar matsala, mafi yawan magungunan da mata ke sha a jihar Kano sun hada da tramadol, codeine, da sauran magungunan tari."
Ta kara da cewa, domin magance matsalolin da suka addabi mata a Jihar Kano, ya kamata a kara wayar da kan jama’a game da illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“Za a iya yin hakan ta hanyar shirye-shiryen makarantu, da taron karawa juna sani na al’umma.
Wani jawabi da Kwamandan NDLEA, Abubakar Idris Ahmad yayi kan ‘tasirin shan muggan kwayoyi ga zaman lafiya da rikice-rikicen al’umma’ ya bayyana cewa: “ shaye-shayen kwayoyi na iya haifar da illa ga zaman lafiya da rikici ta hanyar karuwar laifuffuka, tashe-tashen hankula na kungiyoyi. , tabarbarewar tattalin arziki, da kyama
“Ya zama dole a wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi ta hanyar shigar da makarantu, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauran kungiyoyi.
"Shirin nasiha da nishadantar da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi domin janye tunanin su kan shaye-shyen da suke."
Ya ƙara da cewa NDLEA na hada kai da hukumomin dake yaki da muggan kwayoyi da kuma laifuka masu alaka dasu.
A cikin sakon fatan alheri na Dr. Bashir I Muhammad, Dankaden Kano yace
“Majalisar Masarautar Kano ce kan gaba wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
Ya kuma ba da shawarar cewa, hana buƙatun masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma hana miyagun ƙwayoyi zai taimaka wajen dakile ɓarnar da ake yi.
Ya yi karin haske kan yadda matasa ke amfani da wasu abubuwan da ba su da kwayoyi amma masu illa kamar su zakami, kashin kadangare, kadaji, da kwatami.
"Akwai bukatar samar da dokoki masu sassauci wadanda za su yaki kwayoyi."
Muhimman abubuwan da suka faru na taron sun haɗa da motsa jiki na rukuni da tattaunawa ta mahalarta don yin tunani akan matakai na gaba da tsare-tsaren ayyuka.