Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin rushe gidajen karuwai da sauran guraren aikata baÉ—ala a Maiduguri, babban birnin Jihar, cikin wata ziyara da ya kai unguwar ‘Bayan Quarters’, a ranar Talata, wajen da ake kyautata zaton na dauke da masu aikata laifuka, karuwai da masu safarar miyagun kwayoyi.
Zulum ya umurci hukumomin gwamnati da su tarwatsa su cikin sa’o’i 72, domin ayyukan na kawo barazana ga tsaro da kuma mutuntaka.