Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato wasu jami'an majalisar shari'ar ƙasar, na bayyana haka a lokacin da suka ziyarci ofishinta da ke Abuja.
An dai samu ruɗani kan takardun hukuncin shari'ar da kotun ɗaukaka ƙarar ta yi ranar 17 ga watan Nuwamba a shari'a tsakanin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.
A hukuncin da kotun ta sanar ta soke zaɓen Abba Kabir na NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.
To sai dai bayan fitar da takardun hukuncin, sai wani É“angare na takardun ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne ya yi nasara a hukuncin, wanda mafi yawan bangarensa ke nuna cewa Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara.
Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa a ciki da wajen jihar, tare da jefa shakku a zukatan jama'a.
To sai dai cikin wata sanarwar da magatakardar kotun ɗaukaka ƙarar, Umar Mohammed Bangari, ya fitar, ya ce ya amince da kuskure a cikin takardun hukuncin da kotun ta fitar, to amma ya jaddada sahihancin hukuncin.
Majalisar shari'ar ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafen da suka shafi shari'ar, inda ta alƙawarta duba lamarin kamar yadda dokoki suka tanada.