Jarumar wasan kwaikwayo ta masana'antar Kannywood Hadiza Gabon ta yi karar Bala Musa a kotu, saboda a baya ya zarge ta da karbe masa kudade Naira dubu 396 da sunan za ta aure shi.
Fitacciyar mai harkar fina-finan, ta kuma ce ta kai shi gaban hukuma ne don hakan ya zama izina ga masu irin wannan hali na Bala Musa.