Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin jiha.
Nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala Mni ya yi na radin kansa wanda gwamnatin yanzu ta rike tun daga kafuwarta a watan Mayu, 2023.
Kwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi daban-daban a Kano sama da shekaru talatin, sabon shugaban ma’aikata ya fito ne daga karamar hukumar Kiru.
Abdullahi Musa ya rike mukamin babban sakatare na gidan gwamnatin Kano, daraktan harkokin kansiloli, Admin da General Services of Cabinet Office, Ma’aikatar Aiyuka na Musamman, da Direktan Servicom.
Gwamna Abba Kabir ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan jihar da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a cikin dokokin da suka shafi aikin gwamnati.