Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin CP- Aliyu Abubakar, ta cafke mutum 134 da da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar.
Katsina Reporters ta samu cewa, Kakakin rundunar yan sandan ASP. Abubakar Musa, ya bayyana haka ga manema labarai, a ranar Laraba a Katsina inda ya ce duk a watan Oktoba ne aka kama wadanda ake zargi da aikata laifukan.
A cewar mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Abubakar-Musa, ASP Abubakar Aliyu, ya ce ana zargin wadanda aka kama da laifin fashi da makami da garkuwa da mutane da satar shanu.
Ya ce sauran wadanda aka kama ana zarginsu ne da aikata fyade da safarar muggan kwayoyi da kuma zarginsu da zama mambobi na gungun bata gari.
Acewarsa, cikin laifuka 75 da rundunar ‘yan sandan ta samu an gurfanar da 72 daga ciki.
Da yake gabatar da masu lafuffukan ya bayyana cewa sun kama mutane 13 da ake zargi da fashi da makami da mutum 8 a cikinsu da ake zargi da kisan kai da kuma mutum 39 da ake zargi da aikata ayyukan fyaɗe.
Sai kuma mutum 6 da ake zargi da da mallakar haramtattun ƙwayoyi da kuma mutum 50 da ake zargi da da aikata laifuka da daban-daban da suka shafi tsoratarwa da tayar da hankalin jama'a.
Kwamishinan ya kara da cewa an ceto mutum 23 da aka yi garkuwa da su tare da kwato bingiga daya da harsasai shida da babur daya da sauran kayayyaki.