Wannan ba sabon abu ba ne a kowace siyasa musamman ta jihohi a Najeriya, inda 'yan adawa ke ruguntsimin komawa jam'iyya mai mulki ba tare da wata kunya ba da zarar an kayar da tasu a akwatin zaɓe.
Sai dai abin da ya bambanta ta Kano da sauran shi ne, jam'iyyar NNPP mai mulki da APC mai adawa na cikin fargabar samu ko rasa mulkin yayin da Kotun Ƙolin Najeriya za ta fara zaman sauraron ƙarar da NNPP ɗin ta ɗaukaka.
Bugu da ƙari, APC ta shafe kusan shekara 10 tana mulkin Kano - tun daga lokacin Rabiu Kwankwaso har zuwa shekara takwas na Abdullahi Ganduje - kafin NNPP ta doke ta a 2023. Saboda haka, kowace jam'iyya na ganin kanta a matsayin mai mulki har zuwa ranar da kotu za ta yanke hukunci.
Ɓangarorin biyu za su san makomarsu ne nan gaba a kotun daga-ke-sai-Allah-ya-isa bayan hukuncin kotuna biyu na baya sun soke nasarar NNPP a zaɓen na watan Maris tare da bai wa Nasiru Gawuna nasara a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.
An ga yadda 'yan siyasar suka fara rige-rige wajen gudanar da yanke-yanke da salloli don neman nasara a shari'ar ta kotun ƙoli, wadda ba ta saka ranar yanke hukuncin ba, amma ana sa ran za ta zauna a watan Disamba.
Kazalika, 'yan siysar NNPP da na APC na jefa wa juna zargin bai wa kotuna cin hanci don a murɗa hukuncin ya dace da kowannensu, duk da cewa suna musantawa.
Babu abin da aka fi tattaunawa a kai tsakanin mutane a wuraren zama kamar yanayin siyasar da jiharsu ke ciki, inda wasu ke tausaya wa NNPP wasu kuma ke goyon APC.
Tun daga ranar 17 ga watan Nuwamba - lokacin da kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada nasarar Nasiru Gawuna a hukuncinta - 'yan siyasa da ma mazauna Kano suka shiga cikin zaƙuwa da zullumi.
Hakan ya sa suka shiga gudanar da abubuwa da daban-daban na neman nasara.
Kusan kwana uku ke nan a jere magoya bayan NNPP - waɗanda aka fi sani da 'yan Kwankwasiyya - suna gudanar da zanga-zangar nuna ɓacin ransu ga shari'o'i biyun da suka gabata.
A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen, wata ɗaya bayan haka kuma kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada hukuncin.
"Yancinmu ne [zanga-zanga], duk da cewa jagororinmu sun hana mu, mu kuma mujn ce ba za mu fasa ba wallahi," kamar yadda wata mai zanga-zanga mai suna Fatima ‘Yar Baiwa ta faɗa wa BBC ranar Litinin.
Dandazon ‘yan kwankwansiyya maza da mata ne - sanye da jajayen tufafi riƙe da kwalaye suka yi zanga-zangar a yankin Mariri na ƙaramar hukumar Kumbotso.
A gefe guda kuma, wasu magoya bayan sallah da addu'a suka runguma. Wasu ma har da yanka dabbobi da zimmar Allah ya ba su nasarar cigaba da zama a kan mulkin Kano.
Gomman magoya bayan Kwankwasiyya ne suka taru a mazaɓar Gwamna Abba Kabir da ke Diso Chiranci, inda suka yi salloli da saukar Ƙur'ani.
'Yan APC ba su gudanar da zanga-zanga ba kamar abokan hamayyarsu, amma ba su gaza ba wajen salloli da addu'o'i.
A ranar Lahadi ma, magoya bayan Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC sun gudanar da addu'o'u da saukar al-Ƙur'ani a zawiyar Zawiyar Sheikh Hassan Gawuna.
Haka nan, sun yanka dabba da zimmar Allah ya bai wa ɗan takararsu nasara a mazaɓar tsohon mataimakin gwamnan da ke Gawuna a ƙaramar hukumar Nasarawa.