Babban lauya mai kare hakkin dan Adam a Nigeria, Femi Falana, ya soki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke na soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP, tare da bawa Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC.
Lauyan ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya ce, watsi da kuri’u 165,000 kan rashin yin tambari bai dace ba, bai kamata Alƙalai su hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba.
“Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba. Abin da ya faru kwanan nan kenan a Kano, inda aka ce kuri’u 65,000 da jami’an INEC ba su samu ba.
Muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci, adalci mai yawa, ta yadda ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran INEC ba."