Kasurgumin Dan Daban da Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta Dade tana Nema Ruwa ajallo Mai suna ( Hantar Daba ) Dake kwanar Disu Ya Mika Kansa ga rundunar Yan sandan Jihar ta Kano
Cikin wata Sanarwa da Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya Fitar Yace jiya Litinin matashin ya Mika Kansa zuwa ga Shelkwatar Yan sandan Dake Bompai Bisa rakiyar iyayensa.
Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta Dade tana Neman Dan dabar wanda yaki Mika wuya sakamakon tsarin canja tunaninsu da Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta bullo Dashi
Sai Dai Akarshe Dai Jiya rikakken Dan dabar ya Mika wuya ga Kwamishinan Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel.