Gamayyar ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya na NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta shiga yajin aikin gama-gari sanadiyyar kamawa da kuma dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero.
Ƙungiyar ta sanar da batun yajin aikin, wanda zai gudana a ranar Laraba ne a wata tattaunawa da manema labaru ranar Juma'a, a Abuja.
Shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun kuma bai wa Gwamnatin Tarayya sharuɗɗa shida da suke so a cika, ciki akwai sauke kwamishinan ƴan sanda na jihar Imo, da babban jami'in ƴan sanda na yankin da lamarin ya faru bisa zargin su da hannu a 'cin zarafi da kuma wulaƙanta Mista Ajaero da sauran ƴaƴan ƙungiyar."