A cewar Barr. Abba Hikima ya bada tashi fahimtar dangane da wannan kwafi na takarda daya fita daga kotun daukaka kara wato (Appeal)
Turanci
Without factual basis indicating otherwise, this in my view could pass as a slip since every other part of the judgment is clear that AKY’s appeal has failed. Documents are not read in isolation. We cannot pick and choose.
AKY’s camp should rather invest their energy in the substance and live issues of the appeal than bother needlessly about slips which could be cured and corrected suo motu by the Supreme Court.
Hausa
A fahimtata wannan kuskure ne kotun daukaka kara tayi. Da wuya ka dauki hukuncin kotu ka karanta baka samu kuskure ba. Ba’a zabar wani bangare na hukunci a karanta a manta da sauran. A wannan hukuncin duka sauran bangarorin hukuncin ya nuna AKY bai yi nasara a Appeal ba. Saboda haka, ba za’a dauki wata sadara daya a tsaya a kanta ba. Wannan abu sannane ne a doka kuma doka tayi tanaji na a abunda ake kira “Slip Rule”wanda shine idan an samu kuskure ko tuntuben alkalami a hukunci, to kotu na iya gyara wannan kuskuren musamman idan ma’anar hukuncin ta bayyana.
Saboda haka, gara a bawa ainihin dalilan daukaka wannan kara muhimmanci fiye da wannan.