Mai bawa Gwamnan Kano shawara a bangaren jinkai Fauziyya D Sulaiman ta bayyana cewar, Bayan koke-koke da aka shigar gurin mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf akan masu larurar kwakwalwa da ke yawo akan titunan Kano cikin birni da kauye wasunsu ma tsirara suke yawo, wasu ana cutar da rayuwarsu musamman mata, kuma ba su da galihun da za'a dauke su akai su asibiti,
Gwamnan ya bayar da umarnin a kwashesu akai su Asibitin masu Larurar kwakwalwa domin kulawa da lafiyarsu.
Fauziyya tace Toni suka fara aikin kamar yadda Gwamna yabasu umarni, inda tace fitarsu keda wuya suka sami nasarar kamo wata baiwar Allah "tsirara ta ke yawo akan titi tsahon shekaru abun tausayi, yau dai mun samu daukota da umarnin mai girma Gwamna , sai da likita ya mata allurama sannan aka sakota a mota, kuma insha Allah za mu ci gaba da debosu duk Wanda muka gani suna yawo akan titi"