Wannan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kararrakin zabe tace zabensa mai kammala ba "Inkunkulusib" biyo bayan da abokin karawarsa na Jam'iyyar APC Hayatu Musa Dorawar Sallau, inda ya kalubalanci nasarar Dr Zakariyya.
Wanda ya shigar da shi kotun zabe ta farko wadda kotun ta tabbatar da nasarar Dr Zakariyya na NNPP a matsayin halastaccen dan majalisar kura/garun Malam, wadda daga karshema taci tararsa kudi Naira Dubu 5, hakan yasa Hayatu yayi fatali da hukuncin kotun ya tafi kotun gaba.
Sai dai a jiya ne kotun tace zaben mai kammala ba, dalilin haka dan majalissar maici Hon Dr Zakariyya na Jam'iyyar NNPP yayi kira da al'ummar kura/garun Malam dasu kwantar da hankalinsu.
Inda yace su dufuka da addu'oin samun nasarar na zaben dasuyi anan gaba, "Nasara ta muce ko shakka banayi idan har za'a fito ayi zabe muna kan nasarar, munji ance jama'ar kura/garun malam kunce kundaina zabe sakamakon abinda ya faru koyi hakuri kufito ko kara kare muradinku, ayyuka kuma yanzu muka fara babu gudu babu ja da baya, wannan hukunci bazai sanyayar mana da zuciya ba haryau ni ne nake jagorantarku kuma zamu cigaba da zama akan kujerunmu kafatannin yan Jam'iyyar mu na NNPP, Allah yabawa Gwamnan mu nasara ya kare mana jagoran mu ina godia kwarai".