Hukumar kula da zurga-zurgar ababen hawa ta Kano Karota tayi holin miyagun kwayoyi na kimannin Miliyan 210 da katan din taliyar yara guda 100, Da allura da dai sauransu.
Kakakin Hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na'isa ne ya bayyana hakan a wata ganawa dayayi da 'yan jaridu a Helikwatar Hukumar a wannan rana.
Nabilisi yace cikin abinda Hukumar ta kama harda Magannin karfin maza, da allurar dake gusar da hankali, dama nau'ikan kayan kwalam da makulashe na yara.
A don haka shugaban hukumar ta karota Engr Faisal Muhmud Kabir yake kira da al'umma wajen kula da abinda zasu saya ko naci ko nasha domin tabbatar da cewar basu sayi kayan da wa'adinsu yakare ba, don gudun fadawa barazana ga lafiyar yara dama al'umma baki daya.
Yace ko satin daya gabata sun sami labarin wani daya sha kwaya kuma daga karshe tayi ajalinsa.