Fadar shugaban Najeriya ta ce Faransa za ta dawo wa ƙasar dala miliyan 150 na kuɗin da tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha ya sata.
Fadar shugaban ƙasar ta bayyana haka ne a jiya Juma'a lokacin da shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin ministar Turai da harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, a fadarsa da ke Abuja.
Tinubu ya ce ya ji daɗin labarin dawowa Najeriya kuɗin Tsohon Shugaban kasar mulkin soji Marigayi Janar Sani Abacha da Faransa ke shirin yi, inda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen samar da ci gaba a ƙasar.
Shugaban ya kuma yi farin ciki da irin ƙaruwar hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman ma a ɓangaren sauyin yanayi, ci gaban tattalin arziki, ilimi da kuma raya al'adu.
Tinubu ya kuma yaba da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Yuro miliyan 100 tsakanin Najeriya da Faransa don tallafawa shirin i-DICE - wani shiri na Gwamnatin Tarayya na inganta zuba jari a Fasahar Sadarwa da kuma Masana'antu na Fasaha.
Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Dr Bosun Tijani, da ministan harkokin kasashen waje na kasar Faransa ne suka rattaƁa hannu kan yarjejeniyar a wani taro da aka yi a gidan Tafawa Ɓalewa, a hedkwatar ma’aikatar harkokin wajen.
A nata jawabin, ministar ta ƙasar Faransa ta miƙa sakon fatan alheri na shugaba Emmanuel Macron tare da bayyana shirin Faransa na faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya a ɓangarori da dama.