Ƙungiyar mawaƙan Hausa mai suna Murya Daya, ta barranta kanta daga kalaman da mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya furta a baya bayan nan, wanda ya soki tsohon shugaban ƙasar Nigeria, Muhammadu Buhari, da kuma shaidawa gwamnatin Tinubu cewa, ba zai sake yin irin haƙurin da yayi a baya ba.
Shugabannin ƙungiyar da suka hada da Ali Isa Jita, El-Mu'az Kaduna, Ado Gwanja da sauransu, sun ce bai kamata mutane su yiwa mawaƙan kuɗin Goro na cewa su kamar Karnuka bane, don kawai saboda mutum daya yayi kalamai marasa dadi, wanda kuma ya yisu ne bisa radin kansa.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira, inda ta jaddada cewa, mawaƙa za su cigaba da girmama shugabanni walau su na kan Kujerar mulki walau kuma sun sauka.