Mashiryin shirin fina-finan Kannywood Abdu Amart da aka fi sani da Maikwashe me series din (Manyan mata) ya siyawa iyalin Marigayi Director Aminu S Bono gida a unguwar Dandago kamar yadda maibawa Gwamna shawara akan jinkai Fauziyya D Sulaiman ta wallafa a shafinta na Fasbok.
Tace Abdul Amart ya sai musu gidan kusa da inda Dangin da Yan'uwan Aminu da mai dakinsa suke, yadda yan'uwa za su ci gaba da kula da iyalin nasa a kusa da su, yanzu Iyalan Marigaui Aminu za su taso daga can unguwar da suke domin dawowa gidan da aka sai musu.
Muna adduar Allah ya sakawa Alh. Abdul Amart da alkairi, Allah ya duba zuri'ar shima ko bayan baya raye, Allah kuma ya gafarwa Aminu Bono Amin.