Gwamnatin Jihar Kano ta yi zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya bar mata gadon bashi na sama da Naira biliyan 500.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin taron shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar NNPP a Kaduna, ranar Juma’a.
Aminiya ta rawaito cewa, ya ce suna hasashen idan suka kammala tantance yawan bashin, zai iya haura biliyan 500 din, kuma hakan na kawo wa tafiyar da gwamnatin jam’iyyarsu tsaiko a Jihar.
A cewar sa“Mun karbi mulkin Kano ba mu tarar da komai ba sai bashi. Da farko bashin biliyan 300 ne, amma yanzu ya fara dosar biliyan 500, kuma har yanzu muna ci gaba da tattarawa. Da zarar mun kammala aikin tattarawar, za mu sanar da ’yan Najeriya, musamman Kanawa ainihin yawan bashin domin su san halin da ake ciki,”