Majalisar zartaswar jihar Kano a zamanta na 8 a karkashin jagoranci Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da cire Naira Biliyan 40, domin gudanar da Wasu muhimman ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al'ummar jihar Kano.
Ayyukan sune:
1. Gina gadar sama da ta kasa a Dan Agundi.
2. Gina gadar sama a Sha tale-talen Tal’udu.
3. Inganta hanyoyi tare da gina rufaffun magudanan ruwa a hanyan Jakara - Kwarin - Gogau.
4. Gina titin Kofar Waika - Unguwar Dabai - Yan Kuje Western Byepass.
5. Gina mahadar Unguwa Uku - Yan awaki - Limawa.
6. Kammala hanyar Kanye - Kabo - Dugabau a karamar hukumar Kabo.
7. Kammalawa tare da fadada titin Kofar Dawanau - Kwanar Madugu izuwa hannu biyu.
8. Sake bayar da kwangilar aikin gadojin masu tafiyar kafa, a wurare daban-daban a fadin jihar Kano.
9. Gyaran fitilun kan tituna da fitilu masu bada hannu, dake cikin birni.
10. Karasa biyan kudi tare da dawo da aiki gadan-gadan na kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso a karamar hukumar Madobi.
11. Aikin gyare-gyare a Makarantar Kangararru dake Kiru.
12. Sayan kayayyaki da magunguna domin baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar jama'a damar samar da tsarin kulada masu hatsari, da mata da yara kyauta.
13. Biyan magunguna da sinadarai da kayan masarufi da aka kawo wa asibitin yara na Hasiya Bayero.
14. Kammala biyan kudin shirin gwamnatin jihar Kano zagaye na Uku na allurar rigakafin cutar mashako, a kananan hukumomi 22.
15. Sake gina babban dakin Karatu da ya kone a kwalejin nazarin shari'a ta Aminu Kano.