Wata wasika da Abdullahi Abbas ya rubuta ga Dederi, kuma aka fitar da ita ga manema labarai ranar Lahadi a Abuja, ta ce babban jami'in shari'a na jihar Kano ya zargi shugabannin APC da yin tankwara shari'ar gwamnan Kano a kotun ƙorafin zaɓe ta jihar, da kuma hukuncin alkalan kotun ƙoli da suka kori nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyya NNPP a zaɓen wajen Maris.
Abbas ya ƙara da cewa, kwamishinan shari'ar ya tozarta alƙalan kotun ɗaukaka kara da cewa "bisa ga bayanan da muka samu an yi katsalandan daga masu iko".
“Tun bayan kalaman da ka yi, na samu kiraye-kirayen waya da sakonnin waya masu yawa daga ‘yan uwa da abokai har ma da abokan aikina da abokan arziki suna neman karin bayani a kan ko gaskiya ne jam’iyyata ta yi katsalandan a hukuncin da kotun ta yanke na É—aukaka kara," in ji wasiÆ™ar.
"Na kuma samu barazana iri-iri ciki har da yunkurin kai hari gidana da ke Kano."
Da yake mayar da martani, Dederi ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa bai ga wata wasika daga shugaban jam’iyyar APC ba, yana mai cewa raÉ—e-raÉ—i ne kawai.
"Na ji wasu na cewa, sun gani a shafukan sada zumunta amma ba ni da abin cewa," a cewarsa.