Sojoji hadi da Hukumar Tsaro na Farin Kaya (DSS) sun sami nasarar dakile yunkurin Yan boko Haram na shirin kawo Hari a Jihar Kano.
Sojojin sun ce sun kama ’yan Boko Haram 2 a Gezawa tare da tarin makamai, a kokarinsu na yunkurin kaddamar da wani mummunan hari a Kano.
Abubuwan da sojojin suka kwato daga ’yan Boko Haram da ke kokarin kai hari a Kano,
Sun hadar da bindigogin kirar AK-47 guda biyar 5, manyan bindigun AK-47 masu sarrafa kansu guda biyar 5, na’urar harbo jiragen sama guda daya 1, bama-bamai guda biyar 5, gurneti guda goma 10, kakin sojoji guda biyar sai jakunkunan saka bindigogi guda 10 da kuma wasu sinadaran hada bama-bamai.
Hakan na zuwa ne kwanaki hudu bayan wani harı da Boko Haram din ta kai jihar Yobe da ya salwantar da rayukan mutane sama da 40.