Hukumar samar da abinci da bunkasa noma ta duniya ta ce 'yan Najeriya akalla miliyan biyu da dubu Dari Shida, a Jihohin Borno da Sokoto da Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.
Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin gabatar da bayani na gargadin gaggawa ranar Juma'a a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa bayanin, wani bangare ne na rahoto a kan tabbacin halin wadata al'umma da abinci, da kuma hasashe game da halin da za'a shiga nan gaba.
A cewarsa, halin da ake ciki yanzu ya faru ne bayan wata damuna da ba a saba da ganin irin ta ba,
Wadda aka samu matsaloli da dama, wanda suka haɗa da ta'azzarar halin rashin tsaro kamar rikicin ƴan tayar-da-ƙayar-baya da na ƴan fashin daji.