Babban Lauyan Abba Kabir Yusuf, Olanipekun SAN, ya tashi a gaban alkalai ya gabatar da kokensa kamar haka :
i- Olanipekun SAN, yana neman kotu ta jingine dukkan hukunce hukuncen da kotun Tribunal tayi, musamman wajen zaftare kuri'u 165,000 da akayi wa wanda yake karewa, inda ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wata kotu walau ta Appeal ko ta Supreme da ta taba zaftare kuri'un da aka kama da laifin rashin stamfin INEC.
ii- Koke na biyu da Olanipekun SAN, ya gabatar shine yana ganin akwai kuskure a ayyana Nasiru Gawuna a matsayin Gwamnan Kano tunda a karar da Jam'iyyar APC ta shigar a kotun tribunal babu sunansa a jerin wadanda ke kara.
Babban Lauyan dake kare Jam'iyyar APC, wato tsohon ministan shari'a a tarayyar Nigeria Cheif Akin Olujunmi SAN ya tashi domin bada ba'asi akan wadancan korafe korafen na Olanipekun SAN.
i-Akan batun Kuri'un bogi, Olujunmi SAN, yace ai tun a shekarar 2009, kotunan Appeal suka fitar da hukunci akan kuri'u marasa stamfi tun a wancam lokacin alkalai suka bayyana matsayar su akan cewa rashin yin stamfi da kwanan wata a bayan kuri'a yana daidai da rashin cika ka'idar Hukumar zabe.
ii- A dangane da ayyana sunan Nasiru Gawuna a matsayin wanda yayi nasara duk da kasancewar baya cikin jerin wadanda sukayi karar, Akinwumi SAN yace ai duk kuri'un da aka zaba, da ma duk wani hukunci da aka zartar akan jam'iyya to ya shafi dukkanin yayan jam'iyya, a don haka babu laifi don ayyana Nasiru Gawuna a matsayin Gwamna tunda shima dan jam'iyya ne.
iii- Akinwunmi SAN ya bukaci Kotu da tabbatar da hukuncin cewa Abba ba dan jam'iyya bane a lokacin da aka gabatar da shi a matsayin dan takarar NNPP.
Daga karshe dai kotu ta sallami kowanne bangare, sannan ta sanar dasu cewa zata sanar dasu ranar da zata gabatar da hukunci.
Wannan shine tsarabar da na kawo muku a takaice.