Amma maganar gaskiya shine, zai yi matukar wahala a yanke hukuncin Kano yau duk da cewa kotun koli tasha yin hakan a wasu shari’un.
A fahimtata, shariar Kano, akwai sarkakiya da yawa wadda ake bukatar nazari da warwaresu. Misali, kwan-gaba-kwan-bayan da aka samu a hukuncin kotun daukaka kara kadai na bukatar bayani. Sannan Kano babban gari ne a Nigeria. Akwai manyan lauyoyi a wannan sharia, duka wadannan abubuwan dubawa ne. Allah ya tabbatar wa da mutanen Kano alkhairi". cewar Barr Abba Hikima