Wata takardar kotu da BBC ta gani mai ɗauke da kwanan watan 29 ga watan Nuwamba, na cewa mai ɗaukaka ƙarar yana ƙalubalantar ɗaukacin hukuncin da kotun ta yanke a Abuja, amma ban da ɓangaren da ya ba shi gaskiya.
A baya ma, jam’iyyar NNPP ta shigar da irin wannan kara a gaban kotun kolin, tana kalubalantar hukuncin karamar kotun a kan zaben gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris.
Takardar kotun mai dauke da sa hannun jagoran lauyoyinsa, Chief Wole Olanipekun, ta nuna cewa: Gwamna Abba Kabir na neman kotun - wadda ake yi wa kirari da cewa ‘Daga Ke Sai Allah ya Isa - ta saurari Æ™arar da ya É—aukaka.
Haka zalika, ya nemi ta kori Æ™orafin jam’iyyar APC, sannan ta ba da umarnin tabbatar da zaÉ“en mai É—aukaka Æ™arar a matsayin halastaccen É—an takarar da ya ci zaÉ“en gwamnan jihar Kano na 18 ga watan Maris.
Kotun ce damarsa ta Æ™arshe a shari’ance ta Æ™alubalantar jerin rashin nasarar da ya samu a gaban kotuna har guda biyu, tun bayan kammala zaÉ“en wata takwas da suka wuce.
Hukuncin kotun sauraron Æ™orafin zaÉ“e da na kotun É—aukaka Æ™ara dukkansu, sun bai wa jam’iyyar APC nasara ne, kuma suka umarci hukumar zaÉ“e ta bai wa É—an takararta, Nasir Yusuf Gawuna shaidar cin zaÉ“e.
Abba Kabir Yusuf dai ya gabatar da hujja 28 da yake fatan za su zama madogara a gaban kotun ƙoli.
Daga cikin hujjojin akwai batun cewa Æ™aramar kotu ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke game da wani shaida da aka gabatar mai taken PW32, mai suna Dr Aminu Idris Harbau, abin da ya janyo soke Æ™uri’unsa 165,616.
Abba Kabir yana cewa hujjar da shaidan ya bayar ba ta iya tabbatar da cewa Æ™uri’un ba su da inganci ba.
A cewar takardar Æ™arar Æ™uri’a 3,936 ne kawai ba su da hannu.
Wata hujjar kuma ta yi magana ne a kan hukuncin da ya ayyana cewa Abba Kabir Yusuf ba É—an jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya shiga zaÉ“en 18 ga watan Maris.
Yana mai da’awar takardar rantsuwa mai tabbatar da ingancin bayanan da ya gabatar wa INEC a kan takararsa da katinsa na zama É—an jam’iyya, sun isa shaida.