Baba Ari ya bayyana hakane a wata ganawa dayayi da Jaruma Hadiza Gabon, Inda yace yanzu takai takawo idan yakira Ali Jita baya daukar wayarsa koda kuwa kira nawa zaimasa.
Ali Jita mutumina ne ada amma yanzu yaci moriyar ganga yayarda kuranta, nine nake masa murya akan sautin wakar sa wacce take da tasiri acikin wakokinsa na biki ko na nishadi.
Zuwa yanzu a cikin fina-finan series babu wani mashiryin fim ko mai bada umarni daya taba gayyata ta domin nataka rawa a ciki, sai fim daya kacal mai suna "Gidan Dambe".