Inda yace sunyi aikin da hannu zai ta6a ido yagani, kamar Gine-gine a yankunan, kula da marasa lafiya, samarwa matasa ayyukanyi, haskaka yankunan kura/garun malam, dauwamar musu da wutar lantarki a garin kura, habbaka noma ta hanyar samar musu tallafi daga Gwamnatin Jiha, da dai makamatan su.
Yace a lokacin da suka karbi kujera daga hannun dan jam'iyyar adawa babu abinda zaku iya cewa sunfara, face kawai tallafin baruka guda biyu kacal daya raba a garin kura, sai kawai dumama kujera da yaringayi babu kai kudiri babu aiki sai cika aljihu,
A don haka su al'ummar kura/garun malam sunga canji ta ko ina babu kama hannun yaro, "Dr Zakariyya Alhassan Ishaq bangon sukari ne shi kowa ya dafa sai ya lasa" kuma al'umma sun tabbatar da cewar yau tafi jiya sakamakon arzikin kenkesar kwan Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso.
A don haka ko shakka bamayi jam'iyyar NNPP zatayi nasara a karamar hukumar kura/garun malam da cikin yardar Allah, kuma muna addu'ar Allah yabawa Alh Abba Kabiru Yusuf nasara a "Kotun Surufun"