Amirka ta bai wa Isra'ila tallafin manya-manyan bama-bamai da ke da karfin fasa ramukan karkashin kasa a yankin Zirin Gaza, inda kungiyar Hamas ke yaki da makamai. Mujallar Wall Street Journal ce ta fitar da wannan labari da ta ce Amirka ta fara mika wa Isra'ila wadannan bama-bamai tun kafin barkewar sabon yaki a watan Oktoban da ya gabata.
Mujallar ta ce bama-bamai 100 da sauran wasu makamai sama da 70,000 ne Amirka ta bai wa Isra'ila domin yakar kungiyar Hamas da ke labewa a cikin ramukan karkashin kasa a yankin Zirin Gaza.
Wannan na zuwa ne a yayin da aka shiga rana ta biyu da dakarun Isra'ila suka ci gaba da barin wuta a Gaza tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda. Ma'aikatan kiwon lafiya a wani asibitin Gaza sun ce kusan mutum 200 ne aka halaka tun bayan dawo da ci gaba da hare-hare a baya-bayan nan.