Jami‘an tsaro a jihar Kano na kokarin murkushe barazanar Yan Daba a yankin Karamar Hukumar Gwale dake birnin Jihar.
Rikicin ya dauko asali ne bayan da shugaban karamar Hukumar Khalid Ishak Diso yayi yunkurin shiga Ofis biyo bayan umarnin da wata kotu ta bayar na mayar dashi bayan da majalisar dokokin jihar ta dakatar dashi.
Har wannan lokaci dai yan daba da jami’an tsaro na tsaye a harabar karamar Hukumar bayan da yunkurin Jami‘an tsaron na tarwatsa yan bangar ya ci tura.
Karamar Hukumar Gwale na daga cikin kananan Hukunomin birnin Kano da suka fi fama da rikicin Daba, ita ce mahaifar gwamnan Kano Abba Kabir Yusif na jam‘iyyar NNPP da kuma Abdullahi Abbas shugaban Jam‘iyyar APC.