Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman ya shaida wa gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis cewa jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro ne suka kashe ‘yan fashin dajin.
Ya ce aikin hadin gwiwar ya zo ne bayan korafe-korafe da mutanen yankin suka yi wanda ya kai ga yi wa ƴan fashin kwanton bauna tare da kashe su.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, amma dai ana zargin masu garkuwa da mutane ne, daruruwan su sun kai farmaki kauyen Tonti da ke karkashin gundumar Maihula cikin karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
"‘Yan bindigan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 5:30, kuma suka fara harbe-harbe,” kamar yadda ya shaida wa Channels.
“Da samun bayanai, kwamishinan ‘yan sandan Taraba, Joseph Eribo, ya bayar da umarnin tura wata zugar jami'an tsaro daga reshen Bali zuwa yankin ciki har da hadin gwiwar sojoji da ‘yan banga, da mafarauta."
Ya ce suna ci gaba da farautar 'yan ta'addan da suka tsere, kuma an tura wata runduna ta musamman domin inganta tsaro a yankin.
Sai dai ya kara da cewa: "Wani abin takaici shi ne ‘yan bindigan sun harbe mutanen yankin 12 kafin jami’an tsaro su isa".