A Najeriya, har yanzu ana fargabar yaduwar rikici a jihar Kano bayan da wasu ‘yan banga suka cinna wa majalisar karamar hukumar Gwale wuta.
Har yanzu ‘yan dabar na tsaye suna kallon kallo da ‘yan sanda, kamar yadda wakilinmu na Kanon ya ruwaito mana.