Mai girma Kwomishinan yada labarai na Jihar Kano, Hon Baba Halilu Dan Tiye, ne yayi wannan jawabi, yayin daya karbi bakuncin Mai rike da mukamin Mataimakiyar Manajan Darakta ta gidan Talabijin din ARTV Hajjiya Hauwa Isah a ofishin sa.
Mai girma mataimakiyar Manajan Daraktar tazo domin tanuna masa shedar takardar kama aiki da Mai girma Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya bata.
Baba Halilu Dantiye yace lallai ansaka kwarya a gurbinta, inda kuma yabayyana farin cikin sa, sannan yayi Mata Addu'ar fatan Alkairi da samun nasara a aikinta da zata shiga ofis a ranar litinin mai zuwa.