Dan majalisa Yusuf Shitu Galambi ya fallasa yadda Shugaban ƙasa Tinubu ya gabatar da fankon akwatun kundin kasafi, illa jawabi da yayi musu a baki kawai.
Galambi wanda ya fito daga jihar Jigawa, ya ce a tarihi ba'a taba ganin hakan ba, shi yasa abin ya basu mamaki, domin babu rubutattun bayanai na kasafin da aka warewa kowacce ma'aikata.
Ya ce wasu daga cikin yan majalisar sun tambayi shugabannin majalisar, amma kuma babu wani gamsashshen bayani, kamar ma basa so al'umma su san halin da ake ciki.