Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ce babu wanda ya isa ya yi masa gorin Kano, domin matansa biyu da 'ya'ya 9, duk ’yan jihar ne.
Domin haka shima cikakken dan jihar ne, wannan na zuwa lokaci ne da wasu yan jihar suke yiwa rarara gorin cewar ya bar musu jiha ya koma inda ya fito wato katsina.
Rarara dai yayi shura a fannin wakokin siyasa tun zamanin tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, daga nan ne kuma likkafarsa tayi gaba daga wakokin gwamnoni har zuwa ta shugabannin kasa.
Sai dai wasu jama'ar Kano suna gannin baya yi musu kara musamman idan akayi rashin sa'a ya taba muhibbar wanda suke kauna a siyasance