A cewar gwamnatin Alh. Abba Kabir Yusuf, har yanzu tana ci gaba da amfani da asusun nata daban-daban domin gudanar da ayyukanta a Jihar Kano.
Gwamnatin ta ce takardar umarnin rufe asusunta kan diyyar rushe gidaje da shaguna da wasu 'ya'yan jihar suka karbo daga wata babbar kotun Abuja ta bogi ce.
A don haka gwamnatin ta umarci al'ummar Jihar da suyi fatali da wannan maganar mara toshe mara makama.
A baya dai wasu 'yan kasuwa da gwamnatin Kano ta rushe musu shagunan su, wanda gwamnatin tace sun mallaki waje ba bisa ka'ida ba